Maryam Bukar Hassan wadda aka fi sa ni da Alhan Islam a kafofin sadarwa ’yar faitacciyar jarumar fina-finan Hausa marigayya Hauwa Maina ce. Matashiyar marubuciya ce mai rajin ganin matasa sun dogaro da kansu. A zantawarta da Aminiya ta bayyana yadda marigayyar ta yi mata tarbiya tare da horar da ita kan dogaro ga Allah. Sannan ta bayyana yadda take gudanar da gidauniyarta da shirye-shiryen da take gabatarwa da sauran shawarwari ga matasa kan dogaro da kai:

Mene ne takaitaccen tarihinki?

sunana Maryam Bukar Hassan. Ni haifaffiyar Kaduna ce amma ’yar asalin Karamar Hukumar Biu a Jihar Borno ce. An haife ni a ranar 25 ga Disamban 1996. Na yi firamare a makarantar Kwastam da ke Barnawa Kaduna, sai sakandare a Kwalejin Uncle Bado Memorial Kaduna. Sannan na yi halarci Radford Unibersity College da ke Accra a kasar Ghana. Na kammala hidimar kasa (NYSC) a bana, sannan insha Allah idan dana ya kai wata shida, zan fara digiri na biyu.

Yaya kike gudanar da gidauniyarki da kuma gabatar  dashirye-shirye a talabijin?

Kusan aikinmu iri daya ne da mahaifiyata. Sai dai ita tana bangaren fim, ni kuma na zabi shirye-shirye a talabijin musamman na addini, kuma ina yin hikayoyi na karfafa gwiwar mutane musamman matasa da yara. Kamfanina shi ne Deen At Heart Media, kuma muna shirye-shirye a talabijin da rediyo, kuma za mu fara fitar da mujalla wadda zai fito a Disamba. Kuma ni marubuciya ce, kuma mawakiya na zube. Ina zuwa garuruwa, musamman wajen tarurrukan marubuta da sauransu. Sannan ina yi wa kamfanoni talla. Yanzu haka ina da littafin da na rubuta mai suna In the Heart of Silence. Na saki kaset din muryar littafin, amma kuma asalin littafin zai fita a Disamba. Sai  gidauniyar da muka bude tare da kawata mai suna Sabiha Hussaini mai suna Creatibe Kiddies NG, a nan yara tsakanin shekara 8 zuwa 16 muke koya wa rubutu na kirkiri da magana a cikin jama’a. Sannan  muna koya musu yadda za su kaunaci kansu duk yadda Allah Ya yi su. Sannan abin da ke hannunsu shi ne nasu. Da wasu abubuwa da yawa da muke koya musu.

Cewa kin yi karatu a waje, wadansu na ganin fita waje sai a hankali, amma ga shi har kina koyar da yara tarbiyya da addini, me za ke ce?

Gaskiya ina godiya ga Allah kuma ina godiya ga iyayena musamman mahaifiyata kan yadda ta tarbiyantar da ni. Mama wata mata ce wadda har abin da ba ta samu ba, tana son wani ya samu. Ta saka ni a makarantar Islamiyya har ya kai ina koyar da ita a gida. Kuma ta kasance duk abin da ka sa a gaba, matukar bai saba wa addini ba, takan sa ido tare da taimaka maka hakarka ta cimma ruwa. A Almadina Islamic Academy da ke Kaduna na yi karatun addini.  Sannan abin da ya ja hankalina shi ne bayan mun kammala Islamiyya, sai na ga yawancin kawayena kawai dai sunan sun je Islamiyya ce, amma babu wata alama. Ba sa abin da Islamiyyar ta koyar. Sai a rika cewa wai Islamiyya karantun Lahira ne kawai. Shi ne na ce bari in shiga wannan harkar domin in nuna wa mutane cewa fa lallai duk wanda ya rike addinin Allah, zai ci riba a duniya da Lahira. Sannan in nuna wa mutanen duniya cewa Musulunci ya shafi dukan rayuwar dan Adam. Da na kawo wa mahaifiyata, sai ta ce hakan ya yi kyau domin duk abin da nake yi da kudinta ake amfani, ni kawai sai dai in kawo tsare-tsarena. Haka muka ci gaba, har na bar kasar nan. To kasancewar na riga na samu tarbiyya, sai ya kasance ina so in nuna wa mutane rayuwa kamar littafi ne, kuma kana so a karanta mai kyau. Kuma akwai irin tarbiyyar da ake samu daga gida. Wadansu suna tarbiyyantar da ’ya’yansu su rika jin tsoronsu. Ni kuma tarbiyyar da na samu ita ce in ji tsoron Allah a ko’ina nake. Shi ya sa har yanzu da ba ta nan, Allah Yake ci gaba da min jagora. Shi ne ni ma nake kokarin taimaka wa iyaye wajen tarbiyyantar da ’ya’yansu.

Kin ce ita ce take daukan nauyi, to yanzu yaya kike yi da ta rasu?

Alhamdulillah. Gaskiya mijina yana matukar taimaka min. Tun kafin ta rasu, ya kasance shirye-shiryena suna burge shi, sai shi ma ya shiga harkar. Kuma idan ka yi imani da Allah, zai rika ba ka mafita ta inda ba ka zata ba. To ina godiya gare shi. Kuma dauke mahaifiyata da Allah Ya yi, wani tsari ne daga Allah. Wani lokacin Allah Yakan so Ya nuna cewa wannan fa rainon Shi Ya yi, ba wai wani ba. A ganina, yaya zan yi idan babu mahaifiyta, sai Allah Ya dauke ta Ya ga yaya zan yi din. Amma kuma cikin ikon Allah sai abubuwa suka ci gaba. Gaskiya ina godiya ga Allah da kuma mahaifiyata bisa irin tarbiyyar da ta yi min da kuma mijina.

Kasancewarki ’yar Hauwa Maina yana taimaka a shirye-shiryenki?

Gaskiya na kasance ba na son amfani da sunan wani domin samun daukaka. Tun ina karama nake jin haushin yadda ake tambayar mutum shi dan wane ne idan ya je wani wuri. Tun daga nan na yi alkawarin zan samar wa kaina da sunan da ba sai an tambaye ni ko ni ’yar wane ne ba. Shi ya sa na daina amfani da Maryam Bukar Hassan. Da Alhan Islam nake amfani. Abin da nake so matasa su gane shi ne, idan kana tutiya da iyaye, idan baba su yaya za ka yi ke nan kasancewar yawancin mutane suna yin abu don ganin ido ne? Don haka a wasu wurare idan na je neman abu, ba na fada, kawai ina zuwa ne kamar kowa. Wani lokacin ma har gudu nake yi idan an gane. Amma dai wani lokacin wadansu sukan gane sai su yi min wani abin don tausayi. Amma ni dai ba na zuwa waje da sunan Hauwa Maina. Ina zuwa ne da sunana kawai. Ita kanta kafin ta rasu, idan ta je wani wurin sai ta fada cewa ’yata ce Alhan Islam. Kafin ake sauraronta, saboda a wani wurin idan an santa, a wani wurin kuma ni aka sani. Wani lokacin har mukan yi wa juna wasa cewa idan kike je wuri kaza, sai kin ce musu ke mahaifiyata ce, ita kuma sai ta ce ai nima idan kika je wani wurin sai kin ce ni mahaifiyarki ce.

Yanzu kin cimma manufar gidauniyarki da shirye-shiryenki?

Gaskiya na gode wa Allah. Saboda ka samu mutum sama da dubu 40 sun sanka a duniya baki daya ba Najeriya ba, ai sai godiya. Sannan muna da whatssapp group guda 4 saboda sauran sun cika. Domin mutanen da suke bibbiyata sun kai sama da dubu 40 a fadin duniya. Muna da rassa a Indiya da Sudan da Amurka da Ghana da Kano da Zariya da Kebbi da Neja-Delta da Kalaba. Domin ina koyarwa a Whatsapp. To ka ga a ce ba kasar Hausa ba kawai, har da yankin Kudu baki daya da kasashen waje an san ka sai ka gode wa Allah, kuma kana bayar da gudunmawa ga addinin Allah, kuma mutanen da suke bibbiyata, har wadanda ba Musulmi ba, suna koyon abubuwa daga gare ni. Ka ga koda mutum bai Musulunta ba, idan har zai koyi wani abu ai an ci riba. Don haka wannan ma kadai nasara ce. Na gode wa Allah

To amma yawancin shirinki na yara ne kuma ga shi yara ba sa shiga kafofin sadarwar zamani?

Yanzu yara suna shiga kafofin sadarwa na zamani. Daga shekara 9 yanzu za ka yaro yana yi. Za ka ana saya wa yaro waya domin wasa, daga nan kuma sai ya fara. Kuma manufar ita ce kasancewar a kafafen sadarwa na zamani din wajen fadakarwar kadan ne, alfasha ta fi yawa. Kuma yara kanana suna shiga. Wannan ya sa nake tarbarsu da sauri. Shi ya sa nake bude shafuka domin fadakarwa domin su zama musu wajen koyon addini da tarbiyya ba lalacewa ba. Sannan su gyaru kafin wani ya bata musu tunani. Ke nan sai kafofin sadarwar su zama musu alheri. Kuma ina gabatar da shirye-shirye a talabijin.

Mene ne shafin naki?

A instagram @Alhanislam. Da an sa za a ga Maryam bint Bukar bint Hassan. Gaskiya na fi yin magana ta instagram kai-tsaye, ban cika yin twitter ba. Akwai kuma Deen At heart help line, wato layin lambar da muke taimakon mutane da suke cikin matsala. Akwai lambar a cikin instagram da za a iya dauka.

Da wane harshe kike gabatar da shirye-shiryen?

Ina yi da Hausa da Ingilishi, amma na fi yi da Ingilishi.

Kina da kira ga matsa kamarki?

Mu tashi mu zauna da kafafunmu. Mu daina tunanin sunan iyaye. Kai mene ne idan babu su? Wannan zai ba ka karfin gwiwa da juriya. Kuma karayar arziki na iya zuwa. Don haka kai wane ne ke nan? Don haka a dage a nema, kada a dogara da kowa sai Allah. Duk kalilan da ake samu, a nemi albarkarsa a wajen Allah. Ina yin shirye-shiryen ne sai  in ga gidajen talabijin. Amma yanzu babu wanda ake nunawa, sai dai a manjahar youtub wato deen_at_heart.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here