Jarumin film Lawal Ahmad sananne ne kuma  ya dade a Masana’antar film ta kannywood,  Dan yana daga cikin yaran Ali Nuhu na farko-farko da suka samu daukaka bayan Margayi Ahmad S Nuhu.

Lawal tare da iyalinshi

Yanzu haka Jarumin yana bikin cikarsu shekara 10 da aure shida Matar sa. Wanda hakan yasa shi a jerin jarumai wadanda suka dade tare da matayensu, irinsu Ali Nuhu,  Sani Danja da dai sauransu.

Lawal tare da yaranshi

Lawal Ahmad da Matarsa Allah ya albarkace su da yara Uku, biyu maza daya mace.

lawal Ahmad Wanda dan asalin garin Bakori ne a jihar katsina yayi niyyar fitowa takara a zaben 2019 a matsayin Dan majalissar tarayya mai wakiltar Bakori da Batsari Allah bai Nufa ba.

Lawal da yaransa

Lawan Ahmad yana da kamfaninsa wanda yake shirya finafinai aciki,  sannan yana fitowa a cikin finafinan wasu.

Ubangidansa Ali Nuhu yana daga cikin mutane na farko-farko da suka fara taya su murnar cika shekara 10 A shafinsa na Instagram

Daga Filmhausa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here