Kowa ya kwana ya tashi yasan da sanin cewa kannywood ta rabu gida biyu,

Inda wasu bagare suke goyon bayan shugaba muhammdu Buhari yayin da wasu kuma suke goyon bayan Atiku Abubakar.

A jiya ne wasu daga cikin masu goyon bayan Atiku Abubakar don suka kai masa ziyara a gidan sa daga Yola Jihar Adamawa.

Daga cikin su akwai mai gayya mai Jam’a Fati muh’d,  Abba El mustapha,  Aminu Momoh,  Zaharaddin Sani, Adam M Adam, Isah A Isah sai kuma Dattijo Balarabe Jaji. Da sauransu.

An gano dai Jaruman suna zaune ne a kasa a dan wani karamin parlour  Yayinda shi kuma Atiku Abubakar yake kan Kujera wanda hakan ya zama wani abun gori ga sauran takwarorinsu wadanda suka kaiwa shugaban kasa ziyara inda suka cewa su akan kujera suka zauna.

Kalli Videon dake sama,  Ga wasu Hotunan kuma.

Atiku tare da sauran yan kannywood
Zaharadden sani a zaune tare da yan’uwansa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here