JARUMA FATI MOHAMMED TA FARA YIMA YAN FIM DAUKI DAI-DAI DAGA TAFIYAR BUHARI ZUWA TAFIYAR ATIKU.

Bayan Jaruman masana’antar shirya fina finan Hausa dake Arewacin Najeriya Kannywood sun tabbatar tare da jaddada aniyar bayar da cikakken goyon baya ga shugaban kasa Muhammad Buhari, musamman a zabukan shekarar 2019 dake tafe.

A saboda haka ma Fadar Shugaban kasa ta gayyaci jaruman maza da mata don nuna jin dadi goyon bayan daga gare su har ma suka karrama su da Lambobin girmamawa.

To sai dai rahotanni sun bayyana karara cewar Jaruma Fati Mohammed, tana yima Jaruman masana’antar dauki daidai suna sakin tafiyar Shugaban kasa Muhammad Buhari dake APC, suna kama ta Dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, don har hotunan ziyarar da take kaiwa jaruman sun fara bayyana a kafar soshiyal midiya.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar yanzu haka Jaruma Fati Mohammed tayi nasarar chanza wa wasu daga cikin Jaruman akalar tunani.

Dama chan dai wasu jarumai suna ta korafe korafe kan cewar lokacin tafiya fadar shugaban kasa tafiya aka yi aka bar su hasalima basu da labari suma dai kawai hotunan ziyarar suka gani a kafafen sada zumunci na zama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here