Rahama Sadau

A rana irin ta yau 7 December Jaruma Rahama Sadau take bikin kara shekara,

A wannan Shekarar ma kamar shekaru uku da suka wuce  Jarumar tana wannan biki ne a kasar Cyprus inda take karo karatu,

Rahama Sadau

Da yawa daga cikin masoyanta sun damu  sosai na rashin ganinta a cikin fina-finai akai-akai kamar dai yanda aka saba, haka duk ya faru ne dadlilin karo karatun da Jarumar takeyi ita da kannenta a kasar turai wato cyprus.

Rahama Sadau tana bikin cika shekara 25 a duniya, da dama daga cikin mutane sukan yi mamaki idan suka ji shekarunta musamman irin daukakar da ta samu a wadannan kananan shekarun, wanda wasu daga cikin wadanda suka girme ta ma basu samu hakan ba.

Rahama Jaruma ce mai faran-faran da masoyanta sannan bata da girman kai,  wanda wannan shine sirrin daukakarta.

Rahama Sadau

Jarumar itace ta biyu a gidan su tana da Kanne Guda uku mata sai namiji daya,  sannan akwai babban yayan su Haruna Sadau.

Muna mata fatan Alkhairi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here