Jaruma Rahama Sadau ta kammala karatun makarantar gaba da sakandire wati Jama’a a kasar Cyprus.

Rahama da kannenta
Rahama tare da abikan karatun ta

Rahama ta samu shedar kammala Digirinta ne bayan shafe a kalla shekara uku tana karatun.

A duk wannan tsawon lokacin Jarumar bata daina fitowa a fina-finai ba, musamman na turanci wanda akeyi a kudancin kasar nan. Takan yi amfani da lokutan hutu.

Ta samu wannan shedar ne bayan da ta kammala karatun Diplomar ta a Makaratar Kaduna Polytechnic.

Yanzu dai zamu iya cewa Jarumar ta kere sa’a, domin a cikin Jaruman kannywood mata ba kowacce bace take tsayawa tayi karatu yanda yakamata har takai matakin Digiri.

Kannenta Zainab, Aisha da kuma Fatima Sadau duka suna karatu a makarantar wadda take a kasar Cyprus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here