ADAM A ZANGO YA BAR BUHARI YA KOMA ATIKU

Yanzu dai ta tabbata Zango yabar tafiyar Shugaba Buhari Inda yakoma goyon bayan Atiku.

A dazu ne dai muka bayyana a shafin mu cewa Zango zai bar tafiyar ta buhari

Zango dai bai bayyana dalilan sa na barin Buharin ba, sai dai ya bayyana cewa yabar tafiyar Buhari shi da Jama’ar shi. Wanda suka hada da Fati washa, Zainab Indomie, Isah ferozkhan, Mansur Makeup, da dai sauransu.

Zangon yace ra’ayinsa ne kuma bai hana kowa yabi ra’ayinsa ba.

Zango da Aisha Buhari a villa a watannin da suka wuce

Sai dai a tattaunawar da filmhausa tayi da wani mai goyon bayan Jarumin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, yace ” Zango duk abunda ake mai muna tare dashi yan’uwansa yan kannywood su zageshi su ci masa mutunci amma muna tare dashi, sai dai a wannan karon ya taro ruwan dafa kansa domin ba wani wanda zai zabi Atiku saboda Adamu”

Ya kara da cewa ” Wato abunda Jaruman finafinai basu gane ba shine an wuce lokacin da zakaje acika maka aljihunka da kudi da gida da mota sannan ka fito kace mu zabi wanda kake so ”

Ko ya wannan mi’ara koma baya da Zangon yayi kwanaki kadan kafin zabe zai amfani PDP da Atiku?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here