MATA SUN FI MAZA YAWA A KANNYWOOD KUMA MATAN KANNYWOOD NA YANZU BASU DA KUNYA

Tsohuwar Jarumar masana’antar shirya fina finan Hausa Fati Muh’d, ta ce yanzu haka Jarumai mata sun fi Maza yawa a masana’antar shirya fina finai na Kannywood, wasu ma bata san su ba.

Jaruma Fati Muh’d, tace Yan matan Kannywood yanzu basu da kunya kiri kiri zasu hadu da kai a hanya baza su gaishe ka ba, saboda daukar kai da Isa.

Hajiya fati

Tace wani lokaci ma sai an nuna mun su saboda ni ban san su ba, sun yi yawa ko wace Yarinya yanzu idan ta taso sai tace Fim, suna kallo na baza su mun magana ba ko suna so suce basu sanni bane?

Tsohuwar Jaruma Fati Muh’d, ta bayyana haka ne a wata hira da tayi da manema labaru game da matsayar ta kan yadda Kannywood take a yanzu.

Yanzu haka dai Jarumar ta fantsama a harkokin siyasa kuma tana bangaren Jamiyyar adawa ne ta PDP karkashin Jagorancin Alhaji Atiku Abubakar mai takarar shugabancin kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here