Alhaji Tanimu Akawu shahararren dan wasan hausa ne wanda yace yanzu haka yakai shekara Goma sha takwas yana cikin masana’antar kannywood.

A wata hira da akayi dashi a gidan radiyon Human right na garin Abuja, acikin shirin Dandalin finafinai, tanimu akawu yace mata yan film suna bin mazan banza a waje har ma da masu mulki.

Acikin hirar ya bayyana cewa motar Hadiza Gabon kadai zata sayi motar sa guda Goma. Inda yake cewa ” ka duba ka gani motar Hadiza Gabon kadai zata tawa Guda goma saboda EOD ce nake hawa na saye ta da kudi na dan Uzurina,

Ya cigaba da cewa ” ai film yanzu madubi ne na mata, duk matar da zata ce tana son tayi film so take a haskata ta samu kudi,

“Yanzu misali Maryam yahaya kallo kawai tazo yi aka saka ta a film din Mansoor, amma yanzu wayoyin hannunta sun kai na dubu dari takwas da hamsin amma har yanzu a gidan laka suke, kasan ba’a film kadai ta samu wannan kudin ba domin nawa duka ake biya a kannywood din? “

” Ko ni yanzu kace mun ga yar film in aura bazan aure ta ba saboda nasan me yake tafiya, yarinya tun bata da Nono take kallon mu muna yin film amma tazo cikin shekara daya ta samu abunda mu bamu taba tunanin samu ba, taya zatayi ta girmama mu. “

Me Gabatar da shirin Sabitu Garba Mustapha yace wannan fa babbar magana ce yake yi, ko ya tabbatar da abinda yake fada sai ya kada baki yace ” ai wannan abu ne da kowa ya yariga ya sani. “

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here