Fitaccen jarumin fina-finan Hausa Zaharaddeen Sani ya ce ko kadan bai yi mamakin kazafin da tsohuwar jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta yi musu na cewa su biyar sun yi sama da fadi da Naira miliyan 22 da dubu 500 da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ba ’yan fim din Kannywood.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadin da ta gabata ne Ummi Zee-Zee ta yi doguwar wasika mai taken jiga-jigan barayi biyar na Kannywood, inda ta yi zargin jaruma Fati Muhammad, jarumai kamar Sani Danja da Zaharaddeen Sani da Al’Amin Buhari da kuma darakta Imrana da yin sama da fadi da kudin da Atiku ya ba ’yan Kannywood

zaharaddini Sani

Zee-Zee ta yi zargin cewa wadannan ’yan fim biyar kowannensu ya dauki Naira miliyan 4 da dubu 500.

Tsohuwar jarumar ta bayyana cewa a cikin kudinta ne jarumi Zaharaddeen Sani ya ba ta Naira dubu 25, kuma ta ki kira musu hukumar tsaro ta DSS ne saboda mahaifiyarta ta ba ta hakuri.

Sai dai a lokacin da jarumi Zaharaddeen Sani yake tattaunawa da Aminiya ya bayyana cewa dalilin da ya sa bai mayar da martani ba shi ne don ya fahimci talauci da tabin hankali ne yake damun tsohuwar jarumar.

Hajiya Fati

Ya ce, “Hakika kwana biyu ina gida ina hutawa, domin nakan ware kwana biyu don in zauna a gida tare da iyalina duk lokacin da na yi wani muhimmin aikin da zai sa ban kwana a gida na wadansu kwanaki ba, sai aka rika kirana a waya ana ce mini in ya hau Instagram in ga abin da yake faruwa, saboda na kwana biyu ban hau Instagram ba, saboda na zama babu lokacin hakan.”

Ya ce, bayan ya hau ne sai ya ga Ummi Zee-Zee ta yi wani dogon rubutu inda ta “kira mu da cewa mu ne jiga-jigan barayi biyar a Kannywood, sai na duba na ga babu wani varawo a cikinmu, babu wanda ya haura gidan Ummi Zee-Zee ya yi mata sata,

Sani Danja

“Bayan na karanta bayaninta ne sai na ga wurin da ta ce na ba ta Naira dubu 25 ne kacal, wannan batu fa ana magana ne a kan ’yan Kannywood, abin da nake so in tambaya a nan shi ne wace shekara Ummi Zee-Zee ta yi fim dinta na karshe? A bincika shin ’yar fim ce ko tana bin ’yan fim ne? Furodusa ce ko tana fitowa a fim.” Inji Zaharadeen Sani.

Ya ce, Ummi Zee-zee ba ’yar Kannywood ba ce, kuma babu wanda ya gayyace ta zuwa wurin taron, a baya dai ta tava yin wani fim mai suna Zee-Zee, an samu kuxi da fim xin, amma rabon da ta fito a fim an fi shekara 11.

“Jawaban da ta yi babu hankali a ciki, saboda babu wanda ya gayyace ta duk da cewa ta halarci taron, lokacin da ta zo ma an kammala taron, har mun raka su Bukola Saraki da Uche Secondus da Makarfi mun dawo. Mun dauki hoto da masoyanmu. Na shiga mota zan fita ke nan sai na hadu da ita a bakin kofar shigowa wurin taron, ita da wani dan sanda a bayanta rike da bindiga.” Inji shi.

Ya ce, a nan suka gaisa shi kuma tafi hotel bayan ya sanar da ita cewa ai ta makara domin har an kammala taron.

“Daga nan na koma hotel, to akwai baba Balarabe Jaji shi ne mataimakina na kwamitin shirya taro, inda aka bukaci in kawo mutane 50 wurin taron, inda mutum 300 aka gayyata kuma Zee-Zee ba ta ciki, amma a aljihuna na ba ta kyautar Naira dubu 25. Su Aminu Mirrior daga Zaria duk sun zo, su Fati KK kowa ya zo aka ba shi dan ihsani kamar yadda aka ba wadanda suka je Villa ’yan fim wadanda suke APC.”

Ya bukaci mutane su sani ba cewa ba ma Atiku ba ne ya ba da abin ihsanin da aka raba wa wadanda suka halarci taron, “idan za a sa wa Ummi Zee-zee wuka a wuya ba ta san wanda ya ba da kudin ba. Ba ta ma san yadda aka hada taron ba. Kwanana biyar ban kwana a gida duk ba da cewa ina Kaduna matata ma tana Kaduna, duk don taron ya samu yiwuwa.”

Ya ce, a lokacin da yake sallamar mutane ya bar wayarsa ‘silent’, inda a nan Zee-Zee ta rika kiransa har kusan sau 10, inda zai kira wani ne ma sai ya gane ashe ta kira shi.

“Bayan na kira ta sai ta tambaye ni an ce ana raba kudi? Na ce mata akwai abin ihsani da aka bayar, na ce ta samu wanda ya gayyace ta wurin taron ta karbi abin ihsanin da aka bayar. Ashe gayyar sodi ta zo, zuwan kanta ne.

“Bayan mun ci gaba da magana ne na fahimci kamar tana cikin matsi, tana neman taimako, sai na ce mata ta turo wani ya amshi wani abu, ko ta zo da kanta ta karba, a aljihuna na dauki Naira dubu 25 na ba ta.” Inji shi.

Ya bukaci Zee-zee ta dawo masa da kudinsa Naira dubu 25 tun da ita ba almajira ba ce kamar yadda ta bayyana a rubutunta, domin shi ba ya raina kudi, tun da dubu 25 za ta saya masa buhun shinkafa da kuma katan din taliya.

Ummi Zeezee

Ya ce, yana so Zee-Zee ta sani cewa Allah Ya rufa masa asiri a duniya, tun da “ina motar hawa ba daya ba, ba biyu ba, ba uku ba, ba hudu ba, ba kuma biyar ba. Bayan fim ina da sana’ar da take kawo mini miliyoyi, ta tambayi tarihin gidanmu nawa mahaifinmu ya mutu ya bar mini? Ta tambaya gidana na kaina nawa ake sayar da gida a unguwar da nake? Bayan gidan da nake da zama ina da gidaje fiye da 5 a Kaduna don haka ta yi kadan in yi mata sata.”

Ya ce a yanzu rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna suna nemanta ruwa-a-jallo, inda take guje-guje.

Jarumin ya kalubalanci Zee-Zee cewa idan ba tsoro ba ta fito fili su zauna a gaban jami’an tsaro don ta yi bayanin kudinta da take zargin sun ci mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here